Sojojin Kenya sun shiga Somalia

Sojojin Kenya a iyakar Somalia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojojin Kenya a iyakar Somalia

Dakarun Kenya sun tsallaka iyaka sun shiga Somalia, domin fatattakar 'yan tawaye masu kishin Islama, wadanda hukumomin Kenyar ke dora wa alhakin sace-sacen jama'ar da aka yi a kwanakin nan, a kusa da iyakar kasashen biyu.

A makon da ya wuce an sace wasu ma'aikatan agaji biyu, 'yan kasashen waje, daga sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab, aka nufi Somalia da su.

A jiya ne minista mai kula da tabbatar da tsaro a cikin kasar ta Kenya, George Saitoti, ya sanar cewa, kasarsa zata tura sojoji zuwa cikin Somalia, domin yakar kungiyar al Qaeda.

Sai dai wasu 'yan kasar ta Kenya na fargabar cewa, kungiyar ta Al Shabaab zata kafawa kasarsu kahon zuka, idan har Kenyar ta shiga sosai cikin rikicin Somaliyar.