'Yan adawa a Kamaru sun yi kiran zanga-zanga

A kalla jamiyyun adawa 10 ne a Kamaru suka yi kira da a gudanar da zangar gama gari, don nuna kin amincewa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar na kwananan.

Har yanzu dai ana cigaba da kidaya kiru'a a zaben da aka gudanar ranar tara ga watan Oktoba, zaben da ake saran shugaban kasar Paul Biya zai lashe.