EFCC ta kai Danjuma Goje kotu a yau.

Yau hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje a gaban kotu a garin Gombe.

Sanata Dan Juma Goje, wanda Hukumar ta EFCC ta kama a makon jiya, yana fuskantar tuhumce-tuhumce ne bisa laifufukan da suka hada da sace kudaden jama'a da kuma almubazzaranci da dukiyar jama'a.

An ci gaba da jayayya tsakanin lauyoyin dake kare shi da na hukumar ta EFCC, game da hurumin kotun na sauraron karar.

A kwanan nan ma Hukumar ta EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Oyo, Cif Alao Akala da na Ogun, Gbenga Daniel a gaban shari'a bisa zargin aikata irin wadannan laifuffuka.