Dakarun Kenya sun shiga Somalia

Dakarun Kenya sun shiga Somalia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakrun Kenya sun fara kai hari a Somalia

Ministan harkokin wajen Kenya Moses Wetangula, ya tabbatar da cewa dakarun kasar sun shiga kasar Somalia domin fafatawa da kungiyar Musulunci ta al-Shabab.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce kimanin motoci 40 dauke da sojojin Kenya sun tsallaka kasar ta Somalia ta garin Dhobley ranar Lahadi. An kuma ce an ga tankokin yaki.

Kenya na zargin al-Shabab da hannu wajen sace-sacen 'yan kasashen waje a kasar ta.

Amma wani jami'in diflomasiyyar Somalia a majalisar Dinkin Duniya, ya shaida wa BBC cewa idan dai rahotannin gaskiya ne, to sun keta 'yancin Somalia na kasa mai cin gashin kanta.

Ana zargin al-Shabab da kame 'yan kasashen yamma da dama a Kenya inda ake wucewa da su Somalia.

Kai hari ta sama

An kame wasu ma'aikatan agaji 'yan kasar Spain biyu daga sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab ranar Alhamis.

Haka kuma an sace wani dan Burtaniya da wata mata 'yar Faransa daga wani wurin shakatawa na Kenya kusan wata guda da ya wuce, abinda ke barazana ga harkokin yawon bude ido na kasar.

Da yake magana da BBC, ministan harkokin wajen Kenya Moses Masika Wetangula ya tabbatar da cewa dakarun kasarsa sun fara kai hari kan kungiyar al-Shabab.

"Abinda mu ke yi shi ne biyan bukatar rokon da gwamnatin Somalia ta yi mana da kuma kare tamu bukatar kan kungiyar 'yan ta'adda da ke kame wa da kashe 'yan Somalia da Kenya da kuma 'yan kasashen waje masu kawo ziyara."

Wakilin BBC Will Ross, a Nairobi, ya ce akwai rahotannin da ke nuna cewa jiragen yakin Kenya na kai hare-hare a Somalia.

Wani babban kwamandan sojin Somalia Abdi Yusuf, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, jirage sun kai hari kan sansanonin al-Shabab guda biyu.

Sai dai ba a tabbatar da cewa ko jiragen na kasar Kenya ba ne.

"Ba zan iya tabbatar da jiragen yakin ba, amma makwafciyarmu Kenya na taimaka mana ta fuskar soji, kuma burinmu shi ne mu kori al-Shabab daga yankin," a cewarsa.

A yanzu haka kuma rahotanni sun ce dakarun al-Shabab na barin garin Kismayu na gabar ruwa zuwa garin Afmadow domin fuskantar dakarun Kenya da na gwamnatin Somalia da suka kaddamar da hare-hare a kansu a karshen mako.

"Duka dakarun al-Shabaab da ke Kismayu sun kama hanyar zuwa Afmadow a cikin motocinsu," kamar yadda wani mazaurnin garin Ismail Aden, ya shaida wa Reuters.

Karin bayani