Jami'an Somaliya sun soki shigar dakaru kasar

Dakarun sojin Kenya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakarun sojin Kenya

Manyan jami'an diplomasiya na kasar Somaliya sunce duk wani yunkurin sojojin wata kasa na tsallaka kan iyakar kasar don farautar mayakan 'yan tawaye na kungiyar kishin Islama ta al-Shabaab, ya sabawa kasancewar Somaliya a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Jakadan kasar Somaliya a Kenya, Mohammed Ali Nur ya musanta rahotannin dake cewa dakarun kasar Kenya sun tsallaka zuwa Somaliya.

Sai dai wani mutum da ya ganewa idonunsa ya shaidawa BBC cewa ya ga motocin sojin Kenya da jirage masu saukar angulu sun shiga kasar Somaliya.

A ranar asabar ne ministan tsaron cikin gida na Kenya George Saitoti ya sanar da cewa za'a aike da dakarun kasar zuwa Somaliya don yakar kungiyar Al-Shabaab a cikin Somaliya.