Al-Shabaab ta gargadi Kenya

Mayakan kungiyar al-Shabaab
Image caption Mayakan kungiyar al-Shabaab

Kungiyar Al-shabaab ta Somalia ta yi kira ga Kasar Kenya da ta gaggauta janye dakarunta daga Somalia idan tana so ta kaucewa abunda ta kira kazamin yaki.

Hakan dai ya biyo bayan kutsen da dakarun Kenya suka yi ne cikin Somalia a karshen mako.

An bada rohoton cewa tankunan yaki, da daruruwan dakarun Kenya, na cikin Somalia.

Kungiyar Al-shababba din ta fidda wata sanarwa, da a ciki take gargadi 'yan Kenya da cewa kada su bari yakin da akeyi a Somalia ya yadu zuwa kasarsu.

Wakilin BBC yace Kungiyar ta musanta zargin cewa ita ta kitsa sace-sacen mutane da akeyi a Kenya.

Ta kuma ce zargin da Kenya ta yi na cewa kungiyar na yin barazana da jama'ar Kenya wata hujja ce kawai ta shiga Somalia.