Jam'iyyar CDS Rahama ta yi taro bayan samun baraka

Tutar jamhuriyyar Nijar
Image caption Tutar jamhuriyyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, Jam'iyar CDS Rahama ta gudanar da taro a karon farko tun bayan da Jam'iyar ta bada sanarwar korar ministan cikin gida kuma mataimakin shugaban jam'iyyar, Abdu Labo da wasu mukarrabansa biyu.

An gudanar da taron ne a karshen mako karkashin jagorancin Abdu Labo da magoya bayansa.

Jam'iyyar ta CDS Rahama dai ta samu baraka ne tun daga lokacin zaben shugaba inda aka samu sabani akan ko wani dan takara jam'iyar za ta goyawa baya.