An kai kamfanin Shell kara a Amurka

Kotun kolin Amurka ta ce zata saurari wata karar da wasu 'yan Nigeria suka daukaka, akan kamfanin mai na Shell, inda suke zargin sa da cin zarafin bil'adama.

Masu aiko da rohotanni sun ce za'a iya amfani da hukuncin da kotun zata yanke wajen kafa hujja akan ko za'a iya samun kamfanonin Amurka da laifin kisan kiyashi ko ganawa jama'a a zaba a kasashen waje.

Wasu 'yan Nigeria ne da aka kashe 'yan uwansu a a zamanin mulkin soja a shekarun alif-dari-tara-da-casain suka daukaka karar.

A bara wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin cewa baza'a iya samun kamfanoni da laifi a irin wadanannan shari'un ba.