An gwabza kazamin fada a Yemen

Dakarun adawa a Yemen Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun kabilu masu adawa da shugaban Yemen

Akalla mutane 8 sun rasa rayikansu yayin da wasu 30 suka samu raunika akasar Yemen, bayan da aka gwabza tsakanin masu biyayya da kuma adawa da shugaba Abdallah Saleh.

An samu karuwar zullumi a 'yan kwanakin nan a Sana'a babban birnin kasar, yayin da masu zanga-zanga ke ci gaba da kamfe dinsu na korar shugaba Saleh.

Rahotanni dai sun ce jama'a fiye da 850 ne aka hallaka tun cikin watan Fabreru.

Wakilin BBC Jim Muir a birnin Beirut na Lebanon, ya ce a baya-bayan nan an yi ta jefa rokoki a dandalin da aka yiwa lakabi da suna dandalin sauyi da ke tsakiyar birnin sana'a.

Kuma nan ne masu zanga-zanga ke taruwa don neman shugaba Saleh ya sauka daga kan mulki.

Rahotanni sun ce an kashe mutane hudu sakamakon taho-mu-gamar da aka yi a cikin dare a gabashi da arewacin birnin.

A ranar Asabar ma....

An yi ta gwabzawa tsakanin sojojin kasar da ke goyon bayan shugaban kasar da kuma dakarun da ke goyon bayan kabilun kasar, wadanda ke son ganin shugaba Saleh ya sauka daga kan mulki.

Mr saleh dai ya yi watsi da kiraye-kirayen da kungiyar kasashen Larabawa, da ma kasashen yammacin duniya ke yi masa kan ya sanya hannu akan wata yarjejeniya da za ta sa ya sauka daga mulki.

Idan ya sanya hannu kan yarjejeniyar dai to hakan zai sa kada a hukunta shi bayan ya ajiye mukamin nasa.

Fafatawa ta baya-bayan nan dai na zuwa ne bayan wata irinta da aka yi ranar Asabar, inda rahotanni suka ce sojin da ke goyon bayan shugaban sun kashe mutane goma sha biyu.

Masu zanga-zanga sun yi ta kokarin kaiwa ga yankunan da ke hannun magoya bayan shugaban kasar.

A ranar Lahadi dai, shugaba Saleh ya ce masu zanga-zangar na wuce gona da iri, inda ya zargi wani bangare na wata kungiyar Islama da kokarin yin juyin mulki.

Ana sa-ran za a ci gaba da yin matsin-lamba kan shugaba Saleh a makon da muke ciki, a yayin da kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da taro game da batun tsagaita wuta, da ma mikawa ragamar mulki a kasara ta Yemen.

Karin bayani