Hamas ta mika Gilad Shalit

Gilad Shalit Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gilad Shalit

Kungiyar Hamas ta mika Gilad Shalit ga masu shiga tsakanin 'yan kasar Masar, yayinda iyalansa su ka kama hanyar tarbarsa a karon farko cikin shekaru shida.

Tun da fari dai an ga motocin daukar fursunoni na fitowa daga gidan kaso na kasar Isra'ila inda ake tsare da daruruwan fursunoni Paladinawa, wandanda za'ayi musanya da Gilad Shalit.

A jiya ne dai kotun kolin Isra'ilan tayi watsi da yunkurin hana musayar fursunonin da iyalan wasu 'yan Israila suka yi, bisa hujjar cewa Paladinawan da za'a saki ne suka kashe danginsu.

Kungiyar Red Cross a birnin kudus ta ce bangarorin biyu sun saba ka'idar kasa da kasa da ta amince a ziyarci fursunonin da ake tsare dasu.