Shugaba Ellen ta samu goyan bayan Prince Johnson

Wani tsohon shugaban 'yan tawaye mai karfin fada-a-ji a Liberia, Prince Johnson ya ce zai goyi bayan shugaba Ellen Johnson Sirleaf, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da zaa yi a farkon watan gobe.

Da ma dai Mrs Sirleaf din da abokin takararta, Winston Tubman, sun yi ta zawarcin Mr Johnson din, wanda ya zo na uku a zaben da aka yi a makon jiya.

Prince Jonhson ya fadawa BBC cewa ba zai iya goyon bayan Mr Tubman ba saboda ba mutum ne da ke kokarin sassanta 'yan kasar ba.