Rahoto ya ce Dr Fox ya saba tsarin aikin Minista

Wani binciken da gwamnatin Burtaniya ta gudanar ya gano cewa yadda tsohon ministan tsaron kasar, Liam Fox ya rinka gudanar da aikinsa ya saba wa kaidojin aiki gwamnati.

Binciken ya gano cewa dangantakar tsohon ministan da wani amininsa Adam Werrity ta shafi aikinsa.

Liam Fox ya ajiye aiki ne kwanaki bayan anyi ta cece - kuce a kan yadda abokin nasa wanda ba ma'aikacin gwamnati ne ba, ya rinka halartar tarukan ma'aikatar tsaron kasar kuma yayi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da shi.

Wakilin BBC yace a martaninsa, Dr Fox ya ce, ya amince cewa kuskure ne ya kasa fayyace hakkin abokanta da na aikin gwamnti, amma kuma ya ce, yayi farin cikin cewa rohoton bai same shi da laifin cuwa cuwa ko jefa harkar tsaron kasar cikin hadari ba.