Majalisar kasar Girka ta amince da dokar tsuke bakin aljihu a matakin farko

Fira ministan Girka, Goerge Papandreou Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Fira ministan Girka, Goerge Papandreou

Majalisar dokokin kasar Girka ta amince da wata sabuwar doka a matakin farko, ta shawo kan matsalar bashin da ta dabaibaye kasar.

Dokar, wadda a karkashinta gwamnatin Girkan za ta rage yawan kudaden da ta ke kashewa, tare da kara kudaden haraji, ta zo ne bayan da aka sami barkewar tashin hankali a kasar, a kwana na farko na zanga zangar nuna adawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin.

Gobe idan Allah ya kaimu ne majalisar dokokin zata sake kada kuri'a, kamin dokar ta zama cikakkiya.

'Yan sanda a Girkar dai sunyi amfani da borkonon tshohuwa a kan masu zanga-zanga a Athens babban Birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan da wata zanga zangar- nuna adawa da matakan tsuke bakin aljuhun gwamnati ta rikide zuwa tarzoma.

Dubban mutane ne suka shiga zanga-zangar wadda ba'a taba ganin irinta ba a Birnin.

Zanga-zangar dai itace matakin farko na wani yajin aikin sa'aoi 48, wanda tuni ya gurgunta al'amurra a sassan kasar da dama.

Matakan tsuke bakin aljihun da suka hada da kara kudin harajin, an bullo da sune don magance matsalar bashin da ta yiwa kasar katutu