Maniyyata na korafin karin kudin kujera

Image caption Sarkin Musulmi kuma amirul hajj, Alhaji Sa'ad Abubakar

A jihar Sokoto dake arewacin Najeriya, maniyyata aikin hajjin bana sun koka kan abinda suka kira karin kudade babu gaira babu dalili da suka ce hukumar aikin hajji a jihar ta yi, kuma ta yi gargadin cewa duk wanda bai biya ba, ba zai je aikin hajjin ba.

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa na zargin cewar karin kudin wani yunkuri ne na tilasta musu sakin kujerunsu domin a sayarwa wasu daban.

Sai dai hukumar aikin hajji a jahar ta musanta zargin inda ta ce karin ya fito ne daga hukumar aikin Hajji ta kasa.