Matasa na fama da rashin aikin yi - ILO

Matasa a Afrika ta Kudu
Image caption Wasu matasa na sayayya a wani kanti a Afrika ta Kudu

Kungiyar kwadago ta duniya ta yi gargadi game da abinda ta kira: tabon da matasa za su samu a tsawon rayuwarsu, sakamakon rashin aikin yi, ko kuma 'yan kananan ayyukan da ba sa biyan bukata sosai.

A cikin rahoton da kungiyar ta fitar a ranar Laraba, a kan rashin aikin da matasa ke fuskanta, kungiyar kwadagon ta ce, matsalar za ta yi mummunan tasiri a nan gaba a kan rayuwar matasan.

Ta ce za a sami yawaitar zanga-zanga a tsakankanin matasan, kuma matasan za su dawo daga rakiyar tsare-tsaren siyasa.

Sabon binciken ya nuna cewa matasan da basu da ayyukan yi a duniya sun kai miliyan 75, watau kashi 12 da digo 7 cikin dari kenan.

Rahoton ya ce matasan da ke kasashen Tarayyar Turai na daga cikin wadanda wannan matsala ta fi shafa.

Su kuwa matasan kasashen da ke tasowa, a cewar rahoton, su na fama ne da ayyuakan da ba a bayar da albashi mai gwabi.

Matakan rigakafi

Kungiyar kwadagon ta duniya ta ce ta yi amanna yawan mutane marasa aikin yi yafi adadin da hukumomi suka bayana, tana mai bayyana matasan da basu samu aiki ba, da cewa suna fakewa ne da cewa suna karatu ko kuma suna jiran abubuwa su inganta.

Kungiyar kwadagon ta ba da misali da kasar Ireland wacce ta ce adadin marasa aikin yin kasar wato kashi 27 da digo 5 cikin dari zai zarta hakan da kusan kashi ashirin idan da za a yi la'akari da mutanen da ke fakewa.

Rahoton ya yi hasashen cewa a kasashen Girka da Italiya da Burtaniya za a fuskanci rashin aikin yi na dogon lokaci.

Ya ce matasan da basu da aikin yi a kasashen za su ninka sau uku a cikin shekara daya ko fiye.

Rahoton ya kammala da cewa dole ne gwamnatoci su dauki matakan rigakafi na hana matasa tsintar kan su a cikin matsalar rashin aikin yi, in ba haka ba kuwa za su fuskanci bore da karuwar aikata laifuka, da hada-hadar miyagun kwayoyi.

Rahoton ya bayyana marasa aikin yin da cewa ba su yarda da shugabanni ba, kuma tun da haka ne to za su yi ta nuna musu fushinsu ko da kuwa ta hanyar da bata da ce ba.