Tattalin arzikin Afrika zai bunkasa - Inji IMF

Shugabar IMF Christine Legarde Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption IMF ya ce akwai alaka tsakanin tattalin arzikin Afrika da na manyan kasashen duniya

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF), ya ce shekarar 2011 ta kasance mai tagomashi dangane da ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka.

Ya kara da cewa watakila tattalin arzikin kasashen ya fi bunkasa a shekara mai zuwa.

Ya ce hakan na faruwa ne saboda darajar da kayayyakin da ake samarwa a kasashen ke yi a kasuwanni.

Afrika na fitar da kayayyakin da masana'antu ke amfani da su wadanda suka hada da tama da karafa.

Sai dai Asusun ya ce akwai abubuwan da ke kawo cikas ga bunkasar tattalin arzikin kasashen.

'Alakar kut-da-kut'

"Karin da aka yiwa farashin kayan abinci da kuma fetur ya sanya hauhawar farashin wasu kayyakin abin da ke sa mutanen da ke da karamin karfi ke kashe fiye da kudaden da suka ware don sayen wadansu abubuwan," a cewar IMF.

"Koma bayan tattalin arzikin da ake fama da shi a kasashen da suka ci gaba, ka iya yin illa ga na kasashen da tattalin arzikinsu ke da alakar kut-da-kut da na sauran kasashe, kamar Afrika ta Kudu".

Yawancin kasashen na amfana daga kudaden agaji daga manyan kasashe, da masu yawon bude dio da zuba jari da kuma kudaden da 'yan kasashen da ke ciraji ke turawa gida.

IMF ya ce kananan kasashe na fama da matsala ta daban - wacce ta hada da yawaitar hauhawar farashi, don haka suna bukatar kara kudaden ruwa idan har tattalin arzikin duniya ya ci gaba da tafiyar hawainiya.