Najeriya ta kafa wani asusu na musamman

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani asusu na musamman, domin ajiye rarar kudaden da ake samu daga mai - watau Sovereign Wealth Fund, a turance.

A cewar gwamnatin, kafa asusun zai taimaka wajen sarrafa rarar kudin man ta hanyar da ta dace.

Asusun zai kuma taimaka wajen magance matsalolin ba-zata da ka iya tasowa a nan gaba.

Sai dai mafi yawan gwamnonin kasar na kalubalantar kafa asusun, saboda a ra`ayinsu, babu amfanin ajiye kudin, alhali al`umomin jihohinsu na da bukatun da ya kamata a biya musu yanzu haka.