Fursunonin Palasdinawa sun isa garuruwansu

Wasu fursunoni Palasdinawa da aka sake Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu fursunoni Palasdinawa da aka sake

Wasu da aka sake cikin fursunoni Palasdinawa fiye da duba daya da Israila ta yi alkawarin sakinsu a madadin sojinta Gilat Shalit da kungiyar Hamas ta sake, bayan daya shafe fiye da shekaru biyar a hanunta, sun isa garuruwansu a yankin gabas ta tsakiya.

Goma sha daya daga cikin fursunonin da Israilan ke ganin ci gaba da kasancewar su a gabar yammacin kogin Jordan ko kuma a Gaza na da matukar haddari, an tarbe su ne a Ankara babban birnin kasar Turkiyya.

Haka kuma wasu goma sha shida daga cikin fursunonin tuni suka isa Syria inda aka yi musu maraba tare da daga tutuci a birnin Damascus.

Tun da farko fiye da mutane dubu dari ne suka taru a yankin Gaza inda suka yi ta murnar sakin fursunoni Palasadinawan da Israila ta yi a jiya.