'Yan tawaye sun kashe sojojin Turkiyya 26

Sojojin Turkiyya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Turkiyya na fuskantar hare-hare daga 'yan tawayen Kurdawa

Akalla sojojin Turkiyya 26 ne 'yan tawayen Kurdawa suka kashe a wani fada da bangarorin biyu suka gwabza a Kudu maso Gabashin kasar.

Harin wanda ya afku a gundumar Hakkari inda Kurdawa suka fi yawa, shi ne asara mafi girma da dakarun Turkiyya suka yi a cikin shekaru.

A yunkurin mayar da martani, rahotanni sun ce sojojin Turkiyya sun shiga Arewacin Iraqi inda sansanin 'yan tawayen ya ke.

Shugaba Abdullah Gul ya sha alwashin daukar fansa.

Harin ya zo ne kwana guda bayan da wani bam da ya tashi a gundumar Bitlis ya kashe jami'an 'yan sanda biyar da kuma fararen hula uku.

Dubun dubatar mutane

A 'yan kwanakin nan shugaba Gul ya ziyarci dakarun kasar a yankin domin karfafa musu gwiwa.

Yankin ya sha fuskantar hare-hare daga 'yan tawayen Kurdawa.

Turkiyya ta mayar da martani inda 'yan sanda suka kai sumame kan wadanda suke zargi da marawa Kurdawan baya da kuma hare-hare ta sama kan yankunan Kurdawan a Arewacin Iraqi.

'Yan tawayen na neman karin 'yanci ne a Kudu maso Gabashin kasar inda suke da rinjaye, kuma sun kashe jami'an tsaron kasar da dama da fararen hula 17, tun daga tsakiyar watan Yuli.

Dubun dubatar mutane ne suka rasa rayukansu a rikicin tun a shekara ta 1984.

Akwai ma rahotannin da ke cewa dakarun sojin kasa na Turkiyya na kan hanyarsu ta shiga kasar ta Iraqi.

Sai dai wakilin BBC a birnin Ankara, ya ce idan har wadannan bayanai suka tabbata, to babu shakka ba za su yiwa kasar ta Iraqi dadi ba.