Al-Shabab ta ce ta kashe sojojin Tarrayar Afrika 60

Image caption Mayakan sa kai na Al-Shabab

Rahotanni daga somalia sun ce mayakan sa-kai na Al-Shabab sun baje wasu gawarwarki da dama wadanda suke na sojojin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka ne.

Al-Shabab ta ce ta kashe sojoji ne a lokacin wani dauki-ba-dadi a Mogadishu.

An ambato wadanda suka shaida faruwar al'amarin suna cewa sun kirga gawarwaki akalla sittin.

Wasu daga cikin gawarwakin kuma, gungun mutanen da suka fusata sun yi ta jansu a kasa.

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ko su waye mutanen.

An dai ambato Tarayyar Afirkan na cewa an kashe gommai daga cikin sojojinta a Mogadishu yayin da aka ci gaba da fito-na-fito a daren Alhamis.