Yawan jami'an tsaro a Maiduguri ya damu jama'a

'Yan Sanda a Maiduguri

A jihar Borno dake arewacin Najeriya, wasu mazauna unguwannin da suka fi fama da hare-hare a Maiduguri, sun sake fadawa cikin fargaba kan abinda suka kira, karuwar yawan jami'an tsaro a kowanne lungu da sako na unguwannin.

Mazauna unguwannin na London ciki da Bulunkutu, Dala da makwafatansu na kuma zargin jami'an tsaron da kamen wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan rundunar ta JTF ta bada wa'adin mika makamai.

Sai dai kuma Rundunar ta JTF ta ce zargin da ake yi mata ba shi da tushe.

Haka kuma gidaje da motocin mutane na konewa ne a sakamakon bama-baman dake tashi.