Martanin kasashen duniya kan kisan Gaddafi

David Cameron
Image caption Fira Ministan Burtaniya lokacin da yake mayar da martani kan kisan Gaddafi

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon "Wannan shi ne karshen komai. Makomar Libya da mutanenta na cike da kalubale. Ya kamata dukkan 'yan Libya su hadu domin ci gaban kasar.

"Dole mayaka daga bangarorin su ajiye makamansu domin zaman lafiya. Wannan lokaci ne na sasantawa da sake gina kasa. Ba wai ramuwar gayya ba.

"A daidai lokacin da Libya ke shirya wa zabe, kamata ya yi duk wani mataki da zai taimaka wajen ci gaban kasar a tabbata an aiwatar da shi.

"Kamata ya yi dukkan 'yan kasar su samu damar fada aji a harkokin gwamnati.

Lokacin da aka shafe ana bata-kashi, ya kamata ya zama wata dama ta yin adalci ga kowa-da-kowa".

Fira Ministan Burtaniya David Cameron

"Yau rana ce da za a tuna da dukkan wadanda suka dandana kudarsu a lokacin mulkin Gaddafi.

Daga wadanda suka mutu a harin Lockerbie, da sakamakon hare-haren ta'addanci na kungiyar IRA - wadanda Gaddafi ya rinka taimakawa.

"Za kuma mu tuna da 'yan Libyan da suka mutu a karkashin mulkin kama-karya na Gaddafi.

"Yanzu dama ce da za su kafa tsarin demokuradiyya mai dorewa.

Ina alfahari da rawar da Burtaniya ta taka wajen taimakawa jama'ar Libya kwatar kansu daga mulkin kama-karya. Za mu taimaka musu, za kuma mu yi aiki tare da su."

Shugaba Obama na Amurka

Anasa martanin, shugaban Amurka Barack Obama, ya ce kasar za ta yi kawance da Libya bayan mutuwar Kanal Gaddafi, sannan ya ce aikin Nato a kasar "zai zo karshe nan bada jimawa ba".

"Wannan ya kawo karshen dogon lokacin da aka shafe ana zaluntar jama'a - wadanda yanzu ke da damar yanke hukunci kan makomarsu bisa tsarin dimokuradiya.

"Shekaru 40 da aka shafe ana mulkin kama karya sun zo karshe," kamar yadda Obama ya shaida wa taron manema labarai a fadar White House.

Faransa

"Mutuwar Kanal Muammar Gaddafi wani mataki ne na ci gaba a fadan da aka shafe watanni takwas ana gwabzawa, domin 'yantar da Libya.

"Kame birnin Sirte dole ta bude kofar... Tsarin da NTC ta amince da shi na kafa dimokuradiyya, inda dukkan jama'ar kasar za su taka rawa.

"Yanzu lokaci ne na hadin kai da zaman lafiya."

Italy

"Nasar da duniya ta samu na kadawa. A yanzu da yaki ya kare."

Tarayyar Turai

"Rahotan mutuwar Kanal Gaddafi ya kawo karshen kama-karya da muzgunawa jama'ar Libya da aka shafe shekaru ana yi.

A yau Libya ta bude sabon shafi a rayuwarta tare da kama hanyar dimokuradiyya."

Karin bayani