An kame tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi - NTC

Kanal Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi

Wani babban kwamandan dakarun gwamnatin riko ta Libya, ya ce sun kame tsohon shugaban Libya Kanal Mu'ammar Gaddafi.

Rahotannin wadanda ba a tabbatar ba sun zo ne jim kadan bayan da mayakan gwamnatin rikon-kwaryar kasar suka ce sun fafari ragowar magoya bayan shugaba Gaddafi daga Sirte.

An kwashe makwanni ana dauki-ba-dadi a birnin, wanda mahaifar shugaba Ghaddafi ne, inda yake da dimbin magoya baya.

Wasu rahotanni sun ambato jami'an NTC suna cewa an kuma raunata Kanal Gaddafi a kafa.

A baya dai an samu rahoton kame dan Gaddafi Saiful Islam, amma daga baya ta tabbata cewa ba gaskiya ba ne.

Kanal Gaddafi ya karbi mulki ne a Libya a shekarar 1969.

An kuma kifar da gwamnatinsa ne bayan wani bore da aka fara a watan Fabreru.

Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC na farautarsa.

"Kada ka harbe ni!"

"An kame shi. An raunata shi a kafafuwansa biyu," kamar yadda Abdel Majid, jami'in NTC ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

"Motocin daukar marasa lafiya sun tafi da shi."

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wani jami'in NTC, Mohamed Leith, yana cewa an kame Gaddafi a garin Sirte kuma ya samu "munanan raunuka" amma har yanzu yana numfashi.

Wani soja wanda ya ce shi ne ya kashe Gaddafi ya shaida wa BBC cewa Kanal din ya gaya masa cewa: "Kada ka harbe ni!"

Amma wani jami'in NTC Abdel Majid Mlegta ya shaida wa Reuters cewa an harbi Gaddafi a ka, inda aka kashe shi a lokacin da ya ke kokarin tsere wa.

Reuters sun kuma ambato wani kwamanda na NTC, Abdul Hakim al-Jalil, yana cewa an kama mai magana da yawun Kanal Gaddafi Moussa Ibrahim, kuma an kashe shugaban rundunar sojinsa, Abu Bakr Younus Jabr.

Sai dai babu daya daga cikin rahotannin da BBC ta iya tabbatarwa kawo yanzu.

Wakiliyar BBC a Tripoli Caroline Hawley, ta ce ana harba bindigogi sama a birnin domin murna.

Muhimman wurare a birnin Tripoli

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani