Rana ta biyu a yajin aikin Girka

Zanga-Zangar Girka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanga-Zangar Girka

An shiga rana ta biyu na yajin aikin gama-gari a kasar Girka, bayan wata zanga-zanga a jiya Laraba.

A yau ne kuma ake sa ran majalisar dokokin kasar za ta kada kuri'a kan sabbin matakan tsuke bakin aljihu a karo na biyu a kasar, bisa yarjejeniyar da aka cimma da shugabannin kasashen nahiyar turai da hukumar bada lamuni ta duniya.

Sabbin matakan sun hada da zaftare kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma kara haraji don shawo kan matsalar basussukan da suka yiwa kasar kanta.

Masu suka sun ce yin hakan zai kara durkusar da tattalin arzikin kasar ta yadda ba za ta iya biyan basussukan da ake binta ba.