Watanni uku da kaddamar da taimakon yunwa a Somalia

Sansanin jinkai na Dadaab Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sansanin jinkai na Dadaab

Ministan kula da ci gaban kasashen waje na Burtaniya, Andrew Mitchell ya ce watanni uku tun lokacin da aka bayyana cewa fari na addabar al'ummomi a Somalia, har yanzu matsalar na da girman gaske a kusurwar gabashin Afrika.

Ya kara da cewa daruruwan mutane wadanda akasarinsu kananan yara ne na mutuwa a kowacce rana.

A cewar wasu sabbin alkaluman da aka fitar, ana ciyar da fiye da mutane miliyan biyu da dari hudu a yankin da agajin da Burtaniyar ke bayarwa.

Mr. Mitchell ya ce a Somalia kadai, fiye da kananan yara dubu dari hudu ne ke fuskantar barazanar mutuwa.