Matsalar 'yan jiha da baki a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

A Nijeriya wata matsala da ake fuskanta ita ce ta nuna bambanci tsakanin al'ummomi a wasu jihohin kasar inda ake daukar wasu a matsayin 'yan jiha wasu kuma ana daukarsu a matsayin baki.

Hatta a inda aka haifi iyaye da kakanni ana nunawa irin wadannan mutane bambanci. A inda ake nuna bambancin dai, wadanda ake nuna wa bambancin, ba sa amfana da muhimman ayyukan gwamnati ta fuskar tattalin arzki da siyasa da dai sauransu, yayin da ake bai wa wadanda ake wa kallon 'yan jihar fifiko matuka. Su ma dai masana harkar shari'a a Nijeriyar cewa suke yi wannan halayya ta wasu jihohi, karan tsaye ce ga kundin tsakin mulkin kasar, wanda ya jadda 'yanci da kuma daidaito tsakanin 'yan Nijeriya a duk inda suke.

Misalin na baya-bayan nan shine wanda gwamnatin jihar Abia ta dauka na sallamar ma'ikatan da ba na ta ba.

Abun da kuma ya janyo takun saka tsakanin jihar da jihohin yankin da abun ya shafa.

A yayinda kuma a jihar Filato banbanci da ake nunawa tsakanin 'yan kasa da wadanda ake kira baki, ke ci gaba da janyo zub da jini kusan shekaru goma kenan.

Masana kudin tsarin mulki a Najeriya dai sun ce, tsarin mulki kasar ya ambato maganar dan jiha ne kai a bangaren wakilici a Majalisa.