An fitar da sabon hoton Gaddafi kafin mutuwarsa

Kanar Gaddafi bayan kama shi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kanar Gaddafi bayan kama shi

An fito da wani sabon hoton bidiyon da aka dauka da wayar salula jim kadan kafin mutuwar Mu'ammar Gaddafi.

An ga mayakan gwamnatin rikon kwaryar Libyan suna tafiya da tsohon shugaban kasar sun danna bindiga a kansa.

Ana jin muryoyin mutane na yin musu kan ko a kashe shi ko kuma a'a.

Hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya ta ce tilas ne a gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kashe kanar Gaddafi.

Gwamnatin rikon kwaryar ta Libya dai ta musanta yi masa kisan gilla.

Sabanin yadda addinin musulumci ya shimfida, har yanzu gawarsa na ajiye a wani dakin kankara a Misrata.