Za'a gudanar da binciken dalilin mutuwar Gaddafi

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Marigayi Kanal Gaddafi

Mahukunta a Libya sun ce za su gudanar da binciken dalilin mutuwar tsohon shugaban kasar, Kanar Mauammar Gaddafi, idan anjima a yau, domin tantance yanayin mutuwarsa.

Shugabar Hukumar kare yancin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi kira da a yi bincike kan mutuwar Kanar Gaddafi, bayan shaidu sun nuna cewa an kama shi ne da ransa a Sirte ranar Alhamis.

Hukumar ta bayyana wani hoton da aka dauka ta wayar Salula dake nuni da yadda Mu'ammar Gaddafi ya mutun, a matsayin wani abun damuwa matuka, sannan ta kara da cewar an hana kisan gilla a karkashin dokokin duniya, ta ko wane hali.

Haka ma dai kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta bayyana bukatar gudanar da bincike game da musabbabin mutuwar Kanar Gaddafin.

Amnesty International ta yi kira ga sabuwar gwamnatin wucin gadin Libya ta NTC da ta fito ta yiwa jama'ar kasar ta Libya da kuma duniya baki daya, bayani kan yadda aka kashe Kanar Gaddafi.

Har yanzu dai ba'a tantance inda za'a birne Kanar Gaddafi da dansa Motassim ba wanda shi ma aka kashe shi ranar alhamis.

Wani gidan talbijin a Syria mai goyon bayan Kanar Gaddafi ya watsa wasu bayanai daga iyalan Kanar Gaddafi, inda su ke kira da a ba su gawarwakin mutanen biyu.

An dai sanya gwarwakin ne a cikin na'urori masu sanyaya gawa.

Iyalin Gaddafi dai sun ce an yiwa tsohon shugaban kasar da kuma dansa kisan gilla ne, abun da kuma gwamnatin Majalisar rikon kwaryar kasar ta musanta.