Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Yaran da ake haifa da sikila

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Cutar sikila na yin mummunar illa ga bil'adama

Sikila kamar yadda sashen lafiya na BBC da kuma hukumar lafiya ta Buryaniya NHS suka bayyana, lalura ce da ake gado daga iyaye.

Akan gadi cutar ne idan iyayen sun kasance suna dauke da lalatattun jinsin kwayoyin halitta na cikin jini dake rarraba iskar daga huhu zuwa sassan jiki.

A shekarun 1940 ne dai Dr. Ronald Nagel wani kwararren farfesa akan cutar Sikila, a sashen koyan aikin likitanci na kwalejin Albert Einstein dake Amurka ya yi nazari akan rikidar kwayoyin halittar da ke janyo Sikila.

Kamar dai yadda Dr Ronald ya bayyana, yace za'a iya kwatanta ainihin rikidar halittar dake janyo Sikila da samun tuntuben a bangaren sinadari ko jinsi dake baiwa jiki damar tsuro da kwayoyin halittu.

Kuma kowanne bil adama na da wadannan sinadarai ko jinsi biyu da ake gadar daya daga uwa, daya kuma daga uba.

Idan ya kasance duka jinsin da aka gada din na da illa, to ba za su yi aiki kamar yadda masu lafiya ke yi ba, kuma sune suke zama sikila.

Sai dai Dr. Ronald ya ce kasancewar mutum ya gaji jinsi daya mai lafiya, daya kuma mai illa, ba zai zamanto cewa yana da sikila ba, amma dai idan mace da namiji na dauke da jinsin cutar, za su iya haifar yaro da kwayoyin halittu na sikila.

Domin banbance mai lafiya da mai sikila, Dr. Ronald ya yi misali da cewa su kwayoyin halittun mai lafiya, fasalinsu a zagaye yake, kuma suna da taushi ta yanda za su iya sauya fasali cikin sauki domin zagayawa koina a cikin jiki ba tare da wata matsala ba.

Amma su na mai Sikila, suna da tauri don haka basa iya sauya fasali balle su iya ratsawa ta kananan magudanan jini, sannan suna tankwarewa kamar lauje su kuma like a jikin juna, don haka sukan iya toshe hanyoyin jini, su hana iska ratsa zuwa sauran sassa na jiki.

Idan haka ta faru, sai kwayoyin halittar su mutu cikin kwanaki goma zuwa ashirin, wato kafin cikar lokacin da jiki yake dauka ya tsiro da sabbi.