Kalubalen da ke gaban Libya bayan Gaddafi

Libya
Image caption Akwai kalubale a gaban shugabannin NTC

Masu adawa da Gaddafi a Libya sun yi nasara a fagen daga, tambayar a nan ita ce, za su iya samar da zaman lafiya? Kalubalen na da yawan gaske. Dole ne a samar da doka da oda.

Masu adawa da shi sun bar jama'ar Libya a rabe, amma 'yan adawa sun hade. A yanzu Gaddafi ya tafi, akwai yiwuwar rabuwar kan ta rikide zuwa tashin hankali.

A cike kasar take da makamai. Don haka wajibi ne shugabannin rikon su fito da hanyar da za a hana daukar makamai barkatai.

Dole ne kungiyoyin masu dauke da makamai su ajiye makaman na su, kuma a shigar da su cikin sabuwar rundunar sojin kasar.

A kuma farfado da fannin man fetur na kasar domin ci gaba da aiki kamar yadda yake a baya.

Labari mai dadi

Wajibi ne kuma a fito da wani tsari na siyasa wanda zai kai ga rubuta sabon tsarin mulki; dole ne a baiwa jama'ar kasar damar fadar albarkacin bakinsu ta hanyar kuri'ar jin ra'ayin jama'a sannan a gudanar da zabuka masu cike da adalci.

Labari mai dadi shi ne na cewa Libya kasa ce mai dimbin arziki, don haka ba ta bukatar wani taimako na a zo a gani domin yin hakan.

Akwai damuwa a tsakanin kasashen yamman da suka taimakawa 'yan adawar kasar - suna son ganin sabbin shugabannin Libya sun maida hankali kamar yadda suka nuna a lokacin yaki.

A kasashen Yamma babu wanda ke jimamin mutuwar Gaddafi, amma hanyoyin da aka bi wajen kashe shi, na nuna cewa akwai kalubale a nan gaba, idan hukumomin riko basu karfafa ikonsu ba.

Makomar Libya na da muhimmanci - musamman ga kasashen Turai. Batun kare fararen hula shi ne dalilin ya haifar da hare-haren Nato wanda Burtaniya da Faransa suka jagoranta.

Sai dai yawancin Turawan na nuna damuwa kan ci gaba da tashin hankali a Libya, abinda ka iya haifar da kwararar 'yan gudun hijira a yankin kogin Mediterranean zuwa kasashen su.

A don haka nasarar Libya, nasarar su ce, kuma Libyan na da duk goyon bayan da take bukata, idan tana so, dangane da kalubalen da ke gabanta.