Martanin jaridun kasashen Larabawa kan Libya

Al-hayat
Image caption Yawancin jaridun sun goyi bayan faduwar mulkin Gaddafi

Mulkin zubar da jini ya yi mummunan karshe. Wannan shi ne taken babban labarin da wata jarida mai zaman kanta a Sudan mai suna Attayyar ta buga.

Ita kuwa jairdar Al-Intibaha mai goyon bayan gwamnatin Sudan din ta yi wa labarinta take ne da cewa Fir'aunan Libya ya rigamu gidan gaskiya.

Jidda Al-madina

A kasar Saudia kuwa jaridar Jidda Al-madina da ake sanyawa a kafar internet ta yiwa sharhinta take ne da cewa an kawo karshen mai mulkin kama karya, inda ta kara da cewa Mu'ammarul Gaddafi da burbushin 'yan barandarsa sun fadi ba nauyi, inda suka bar duniya a matsayin wani waje mai nagarta da zai kasance ba 'yan mulkin kama karya.

Jaridar ta kara da cewa shugabannin da suka ruguza kasarsu, suka kashe mutanensu sannan suka yi amfani da makamai dan raba kan kasar sune mafiya muni da kuma laifi sama da yan mulkin mallaka da suka bautar da kasashe da kuma hana musu yanci da walwala.

Ad-Dustur

Ita kuwa jaridar Ad-Dustur mai zaman kanta dake goyon bayan gwamnati a aksar Jordan cewa tayi Gaddafi da dansa basu bada wata damaba da za'a tausaya musu.

Ba wai kawai sun ci zarafin yan Libiyaba da kuma yiwa dukiyarsu ta'annati ba ne, bari dai sun kalubalanci abin da jama'ar kasar suke so.

Sai dai duk da haka dakarun juyin juya hali sun yi asarar wata babbar dama ta yiwa Gaddafi doguwar shari'a da kuma jin maganganunsa daga cikin kurkuku.

Jaridar tace ba kamar sauran shugabannin kasashe da suka zabi su mika mulkiba, Gaddafi ya zabi yayi irin wannan karshe.

Al-Ra'ay

Amma shi kuwa gidan Talabijin din Al-Ra'ay na kasar Syria mai goyon bayan Gaddafi a shirinsa na buga waya da safiyar Juma'a cewa yayi, Gaskiya daya da kungiya NATO da 'yan barandanta ba za su iya boyewaba shi ne an harbi wadannan shahidan ne a kirji da kuma kansu, basu guduba kuma basu bada kaiba.

Kuma kisan da aka yiwa Gaddafi da dansa ya tabbatar da matsayinsu a cikin shahidai da tuni biyu daga 'ya'yansa Khamis da kuma Saiful Arab da ma wasu jikokinsa suka rigayesu.

Al-Safir

A kasar Labanan Jaridar Al-safir mai neman kawo sauyi, cewa tayi kashe Gaddafi ba wai ya kawo karshen mulkinsa bane kawai, ya kawo karshen mutumin da idonsa ya rufene wajen tsananin san mulki da kuma hana kowa.

Tace babu laifi yadda 'yan Libiya suka ringa murna suna nuna farin ciki da kisan Gaddafi, sai dai yadda aka ringa nuna hoton gawarsa a akwatunan Talabijin ya sabawa mutuntuka.

Al-hayat

Jaridar Al-hayat mai kishin Larabawa mallakin Saudia da ake bugawa a Burtaniya kuwa cewa tayi, idan dai har banbance-banbancen da ake fama dasu a yanzu haka suka kankane batun kafa sabuwar gwamnati, idan banbancin kabila da kuma fafutukar samaun mukamai tsakanin bangarori masu mabanbantan ra'ayoyin siyasa da suka kawar da gwamnatin gaddafi ya zama shi ne kan gaba.

Sannan idan ko wane bangare bai hakura da wasu bukatunsuba saboda ci gaban kasa, to Libiya za ta shiga sabon rudani fiyema da ace Gaddafi yana raye kuma yana mulkin Libya.