NATO za ta kammala yaki a Libya a karshen wata

Image caption Anders Fogh Rasmussen

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya ce kungiyar ta dauki matakin kammala yaki a Libya a karshen watan Oktoba.

Da yake jawabi jiya Juma'a, ya ce kungiyar za ta yanke shawara ta karshe a mako mai zuwa bayan ta tattauna da Majalisar rikon kwarya ta Libya da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, ya ce kungiyar ta dau matakin daina kai hare-hare a Libya daga ranar talatin da daya ga watan Okutoba.

Ya ce bayan wannan lokacin NATO za ta kara nazari a kan ayyukan ta, kuma za ta yanke shawarar ko za ta ci gaba da kare fararen hula a kasar, idan bukatar haka ta taso ko a'a.

Kare fararen hula

Mista Rasmussen dai ya ce yana farin ciki da irin nasarar da NATO ta samu a Libya.

Ya ce; "Dakarun mu sun hana a yi kisan kiyashi, mun kare rayuka da dama.

"Mu muka samar da damar taimakawa mutanen Libya su sauya makomarsu.

"Bajintar da su ka nuna wajen nemowa kan su yancin za ta zama abun koyi ga mutanen duniya da dama." In ji Rasmussen.

Anders Rasmussen, ya ce NATO ta sauke nauyin da ke kanta, kuma yanzu ya ragewa al'ummar Libya su hada kansu wuri guda su gina kasarsu a kan turbar demokradiya.

Tun farko dai, Majalisar rikon kwaryar ta Libya ta ce za ta ba da sanarwar daina yaki a kasar ranar Lahadi.

Kungiyar tsaro ta NATO dai ta taka muhimmiyar rawa wajen hambarar da gwamnatin Kanar Gaddafi daga kan mulki.

Kungiyar ce dai ta karya lagon sojojin Gaddafi bayan hare-haren da take ta kaiwa ta sama.