Saudiyya: Yarima Sultan Bin Abdul Aziz ya rasu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marigayi Yarima Sultan Bin Abdul Aziz yana magana da wani dan wasa.

Yarima mai jiran gado a kasar Saudi Arabia, Yarima Sultan Bin Abdul Aziz ya riga mu gidan gaskiya a wani asibiti da ke New York, inda ake jinyarsa.

Yarima Sultan Bin Abdul Aziz, ya rasu ne yana da shekaru fiye da tamanin.

Yarima Sultan dai na cikin 'ya'yan Sarki Abdul Aziz Ibn Saud, wanda shi ne ya assasa kasar ta Saudi Arabia.

Ya rike mukamin ministan tsaron kasar har tsawon kusan shekaru hamsin.

A shekara ta 2004 ne dai aka gano cewa yana dauke da cutar sankarar uwar hanji.