An cinma yarjejeniya kan tallafawa euro

Ministocin kudi na kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun cimma wani matsayi da zai kai ga shawo kan matsalar basussukan da wasu kasashe dake amfani da kudin Euro ke fuskanta.

Yanzu dai wajibi ne bankuna a kasashen dake amfani da kudin Euro su daga jarinsu don kare kansu daga mummunan halin da kasuwannin hada-hadar kudade za su iya fadawa ciki.

Hakazalika, ana so bankunan su amince da cewa sun tafka asara mai yawa kan takardun bashi, ko Bonds a turanci na gwamnatin Girka.

Sai dai har yanzu ministocin ba su cimma 'yarjejeniya ba a kan batun fadada amfani da asusun ceto tattalin arzikin dake fama da basussuka ba.