An kai hari a garin Saminaka, jihar Kaduna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Saminaka a jihar Kadunan Nijeriya sun tabbatar da mutuwar mutane akalla biyu a sakamakon hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai a daren jiya kan wani ofishin 'yan sanda da kuma wani banki.

Ba a tantance wadanda suka kai harin ba, amma an ce sun kwashi kudi a reshen bankin First Bank da suka fasa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhaji Bala Nassarawa ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kuma ce suna ci gaba da gudanar da bincike.