An fara zaben yan Majalisa a Tunisia

Image caption Da karfe bakwai ne aka fara kada kuri'a a runfunan zabe.

Yanzu haka dai an fara zaben 'yan Majalisu a kasar Tunisia a karon farko tun bayan boren aka yi wanda ya hambarar da gwamnatin Zine el Abidine Ben Ali.

An dai tunkude Mista Ben Ali ne daga kan karagar mulki, bayan an shafe makwanni ana gudanar da zanga zanga a kasar saboda wani matashi ya cinnawa kansa wuta don nuna adawarsa da gwamnatin kasar.

Za a dai zabi 'yan Majalisa ne wadanda kuma za su tsara sabon kudin tsarin mulkin da zai ba da damar nada sabon shugaba na wucin gadi.

Al'ummar Tunisia dai na zabe ne a karon farko, tun bayan da aka fara bore a kasashen larabawa watanni tara bayan tunbuke Shugaba Zinedine el Abidine Ben Ali daga kan karagar Mulki.

Gwamnatin wucin gadi

Za su zabi 'yan Majalisa dari biyu da goma sha bakwai ne, wadanda kuma za su tsara sabon kudin tsarin mulkin da zai ba da damar nada gwamnatin wucin gadi a kasar.

Jam'iyyar masu kishin Islama ta Ennahda ce ake ganin za ta samu kuri'u mafi rinjanye, sai kuma Jam'iyyar PDP mai ra'ayin raba addini da siyasa ke biye da Ita.

Mista Ben Ali dai ya tsere ne ya bar Tunisia a ranar goma sha hadu ga watan Junairun bana, bayan boren kin jinin gwamnatin da aka gudanar a kasar.

An dai samu 'yan matsaloli wajen Kamfe a Tunisian, musamman ma rarrabuwar kawunan da aka samu tsakanin masu kishin Islama da kuma wadanda ke nema a raba addini da siyasa, da kuma batun kudaden gudanarwa na jam'iyyu.

Akwai akalla mutane miliyan bakwai da shekarunsu suka kai su kada kuri'a a kasar, kuma sama da jam'iyyun siyasa dari ne suke takara a zaben, da kuma 'yan takara masu zaman kansu.

Daruruwan jami'an kasashen wajen da dubban na cikin gida ne za su sa ido a zaben na yau.

Ana kyautata zaton sabuwar Majalisar idan an kafa ta zata tsara sabon kudin tsarin mulkin kasar ne cikin shekara guda.