An bada sanarwar 'yanto Libya

Mustafa Abduljalil
Image caption Mustafa Abduljalil

Sabbin mahukuntan Libya sun bada sanarwa a hukumance cewa sun 'yanto baki dayan kasar daga mulkin tsohon shugaba marigayi Kanar Gaddafi.

An yi bikin bada sanarwar ce a birnin Benghazi a wajen barikokin soja inda masu zanga-zanga suka fara nuna adawa da mulkin Kanar Gaddafi a cikin watan Fabrairu.

Shugaban majalisar wucin gadi ta NTC, Mustapha Adul Jalil, ya duka domin yin godiya ga Allah SWT, bisa nasarar da suka samu kafin daga bisani jamaa su fara shagulgulan murnar wannan nasara.

Mustapha abdul Jalil, ya yi kira na yafewa juna da sassantawa da kuma hadin kan 'yan kasar ta Libya. Ya kuma yi godiya ga dukan wadanda suka shiga cikin juyin juya halin, kama daga mayaka zuwa

'yan kasuwa da kuma 'yan jarida da suka goyi bayan sauyin da aka kawo a kasar.

Ya ce sabuwar kasar Libya za ta yi aiki da shariar musulunci a matsayin tushen manufofinta.