An yi girgizar kasa a gabashin Turkiyya

Girgizar kasa a Turkiyya
Image caption Girgizar kasa a Turkiyya

An yi wata girgizar kasa mai karfin gaske a gabashin kasar Turkiyya, inda gine gine masu dama suka zube.

An tabbatar da mutuwar mutane 50, amma hukumomi suna fargabar cewa adadin mamatan zai zarta hakan.

Girgizar kasar ta fi karfi ne a wani kauye dake kusa da birnin Van.

Mukaddashin praministan Turkiyya, Besir Atalay ya ce gine gine kamar goma sun zube a birnin shi kansa, bayan wasu talatin a yankunan dake kusa.

Gidan talabjin na kasar ya nuna yadda masu aikin ceto, na ta ginar kasa, domin zakulo wadanda baraguzan gini suka binne.

Karin bayani