Burtaniya za ta kada kuri'ar raba gardama kan Tarrayar Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fira Ministan Burtaniya, David Cameron

'Yan Majalisar dokokin Burtaniya za su kada kuri'ar raba gardama idan anjima a yau din nan kan ci gaba da barin Burtaniya a matsayin memba a kungiyar Tarrayar Turai.

'Yan majalisa da dama masu ra'ayin mazan jiya sun ce ya kamata a baiwa masu kada kuri'a damar fada a ji a kan zaman Burtaniya a kungiyar, ko kuma a sake tattaunawa kan dangatakarta da Turai.

Gwamnati Burtaniya dai na adawa da zaben raba gardamar, kuma a yanzu tana fuskantar trujiya daga 'yan majalisa masu ra'ayin mazan jiya.

Bincike dai ya nuna cewa Burtaniya ce kasar da ta fi yin wasuwasi a kan kasancewarta memba a kungiyar tarrayar Turai.

Ra'ayoyin jama'a dai na ci gaba da nuna cewa idan da za a gudanar da kuri'ar raba gardama a yau din akasarin 'yan Burtaniya za su zabi ficewar daga kungiyar ta Tarrayar Turai, fiye da zamanta.

Wannan batu ma haka yake a Majalisar dokokin kasar, inda 'yan Majalisa masu ra'ayin mazan jiya ke ci gaba da nuna adawarsu da zaman kasar a kungiyar.

A yanzu haka dai wata kungiyar 'yan Majalisar masu ra'ayin mazan jiya tana kokarin ganin an kada kuri'ar raba gardama a kan ci gaba da zaman Burtaniya a kungiyar; sai dai Pira Minista David Cameron ya ce ko da yake shi ma yana da dan shakku game da zaman kasar a Tarayyar ta Turai, amma har wa yau bai amince a kada kuri'ar raba gardamar ba.

Ya ce kamata ya yi kasar ta maida hankali, wajen magance matsalolin da ake fuskanta a kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Akwai yiwuwar zaben raba gardamar ba zai samu amincewar Majalisar ba, ganin cewa shugabanin manyan jam'iyyu uku na adawa da shi.

Amma abun sa ido a nan shi ne yawan yan majalisa masu ra'ayin mazan jiya masu adawa da Mista Cameron.

A yanzu haka dai ana ganin kada kuri'ar wani yunkuri ne na gwada iya shugabancin Mista Cameron da kuma yadda ake adawa da tarrayar Turai a Burtaniya.