'An yi wa wasu magoya bayan Gaddafi kisan gilla'

Sirte
Image caption An dai gwabza kazamin fada a garin na Sirte

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights watch ta ce tana da shaidun da ke nuna cewa fiye da magoya bayan tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi 50 ne aka harbe a wani otel a garin Sirte.

Ta ce ta gano wasu gawarwaki 53 da aka tara a wuri guda - wasu daga cikinsu an daure musu hannaye ta baya.

Otel din dai na karkashin yankin da masu adawa da Gaddafi ke iko da shi ne kafin ayi kisan.

Kungiyar ta ce akwai harsasan bindiga a kasa da kuma jini a kusa da gawarwakin.

A gudanar da bincike

A cewar rahoton da kungiyar ta fitar, kusan dukkan mutanen za a iya cewa an kashe su ne a wuri guda - inda ake tsare da su a matsayin fursunoni.

An rubuta sunayen wasu kungiyoyi da ke adawa da Gaddafi a bangon otel din, abinda ke nuna cewa su ne keda iko da wurin.

Mazauna garin sun shaida wa Human Right Watch cewa dukkan mutanen mazauna garin na Sirte ne, cikinsu har da wani jami'i a tsohuwar gwamnatin Gaddafi da kuma wani soja.

Kungiyar Human Right Watch ta yi kira ga shugabannin riko na NTC - da a yanzu suka ce sun kwace kasar baki daya, su gudanar da bincike mai zaman kansa, kuma su tabbata an gurfanar da wadanda aka samu da laifi a gaban shari'a.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa tsohon jagoran na Libya Kanal Gaddafi bayan da dakarun NTC suka kama shi a makon da ya wuce.