An kai hari a wata mashaya a Kenya

Image caption Taswirar Kenya

An jefa gurneti a wata mashaya da ke tsakiyar babban birnin kasar Kenya, wato Nairobi, inda akalla mutane goma sha hudu suka jikkata.

Har yanzu dai ba a san dalilin kai harin ba.

Kungiyar masu kisihin Islama ta Al Shabaab a Somalia dai ta yi barazanar daukar fansa bayan da sojojin Kenya suka kutsa cikin Somaliar don fatattakar mayakan sa-kai.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya bayyana cewa:

"Na ji wata kara, sannan na ga hayaki ya tashi daga nan sai na fadi a sume.2

A cikin Somalia kuma an kai hari ta sama a kan wani sansanin kungiyar ta Al-Shabaab wanda ke daura da tashar jiragen ruwa ta Kismayo.

Sai dai kungiyar ta ce ba a yi mata wani ta'adi ba.