Zaa yi bincike kan mutuwar Gaddafi- Jalil

Mustapha Abdul Jali tare da wasu kwamandojin soja Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mustapha Abdul Jali tare da wasu kwamandojin soja

Shugaban majalisar rikon kwaryar Libya, Mustafa Abdul Jalil, ya bada sanarwar gudanar da bincike game da mutuwar Kanar Mu'ammar Gaddafi.

Mr Jalil ya ce matakin ya biyo bayan damuwar da kasashen waje da ma kungiyoyi ke nunawa ne kan mutuwar tsohon shugaban kasar Libyan.

An dai ga Mu'ammar Gaddafi da ransa bayan da aka kama shi kafin mutuwarsa, wadda da alama ta harbin bindigar da aka yi masa ne.

Mr Jalil ya ce galibin 'yan Libya sun so ne su ga an gurfanar da Kanar Gaddafi a gaban shari'a, kuma tsaffin magoya bayansa ne kawai suke so su ga an yi saurin kashe shi.

Mr Jalil ya kuma tabbatarwa kasashen duniya cewa sabuwar Libya za ta kasance wata kasa mai matsakaicin ra'ayin Islama, duk da cewa tana so ta yi aiki da tsarin shariar musulunci .