Girgizar kasa: Daruruwan mutane sun mutu a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sama da mutane dari biyu sun rasa rayukansu ya zuwa yanzu.

Mutane da dama ne suka mutu sanadiyar girgizar kasar da aka yi a gabashin Turkiyya.

Mahukunta a kasar sun ce an tabbatar da mutuwar sama da mutane dari biyu amma akwai fargabar cewa yawan adadin mutanen zai karu zuwa daruruwa.

A gabashin Turkiyya inda girgizar kasar ta auku, an samu rahotannin da ke cewa an samu wata karamar girgizar kasa a garin Ercis inda kusan gidaje talatin su ka ruguje.

Har wa yau girgizar kasar ta yi muni a birnin Van da ke makwabtaka da garin.

Pira Ministan Turkiyya Rejep Tayip Erdowan, ya isa birnin Van a daren jiya inda ake aikin ceto gadan-gadan.

Ma'aikatan agaji na kokarin zakulo mutanen da gine-gine su ka rufta a kansu.

Hukumar ba da agaji ta Red Cresent a Turkiyya ta samar da tentuna da barguna da kuma abinci ga wadanda abun ya shafa.

Kasar Burtaniya da Amurka sun nuna cewa a shirye su ke domin ba da gudummawa, amma har yanzu kasar ta Turkiyya ba ta yi nuni da cewa ko tana bukatar taimako daga kasashen waje ba.

Wannan bala'indai na kara girma ne, musamman idan aka yi la'akari da cewa yawan mutanen da abun ya shafa na kara yawa.