Ennahda na ikirarin lashe zaben Tunisia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Ennahda, Rashid Ghannouchi

Jam'iyyar Ennahda mai matsakaicin ra'ayin Islama a kasar Tunisia ta yi ikirarin lashe zaben kasar wanda aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.

An gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar ne wadanda za su shatawa kasar sabon kundin tsarin mulki, sannan su zabi shugaban rikon kwarya da zai sanya kasar kan turbar mulkin dimokaradiyya.

Jam'iyar dai ta yi alkawarin samar da tsarin dimokaradiyya mai jam'iyyu daban-daban.

'Yan jam'iyyun adawa sun amince da shan kaye, sai dai sun nuna shakku ga kalaman jam'iyyar Ennahda na barin kowa ya gudanar da addininsa ba tare da shamaki ba.

A yau Talata ne ake sa ran fitar da sakamakon zaben a hukamance wanda masu sa ido akan zabe na kasashen duniya suka ce ya gudana cikin adalci.