An binne Kanal Gaddafi a asirce

Gaddfi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jama'a sun taru domin kallon gawar Gaddafi kafin a binne shi

Mahukunta a Libya sun ce an binne gawar Kanal Gaddafi da ta dansa Mu'atassim da kuma wani na hannun damarsa a asirce a cikin saraha.

Wani jami'in gwamnatin riko ta National Transitional Council (NTC), ya shaida wa BBC cewa an binne gawarwakin ne a wani wuri da ba'a bayyana ba, da sanyin safiyar ranar Talata.

Wannan ya biyo bayan shafe kwanaki da jami'an NTC suka yi, suna tantamar yadda za su yi da gawarwakin mutanen.

Iyalan Kanal Gaddafi sun so a basu gawar domin a binne ta a wajen mahaifarsa da ke garin Sirte.

Sai dai jami'an NTC sun fi son a binne shi a asirce.

'Wurin da ba'a bayyana ba'

Guma Al Gamaty na NTC ya tabbatarwa da BBC binne gawarwakin na Gaddafi da dansa da kuma wani na hannun damarsa.

Tunda farko kamfanin dillancin labarai na AP ya ce ya samu tabbaci a wani sakon text daga wani kwamandan soji a Misrata, cewa an binne mutanen ne a wani wuri da ba a bayyana ba da misalin karfe 05:00 na safe agogon Libya.

Akwai danginsu 'yan kadan da kuma jami'an gwamnatin riko inda aka yi musu salla irinta addinin Musulunci, a cewar mai magana da yawun NTC Ibrahim Beitalmal.

Tun da farko wani jami'in NTC ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa za a binne Kanal Gaddafi a wata "karamar" janaza wacce "malaman addini" za su halarta ranar Talata.

"Zai kasance wani wuri na boye da ba za a bayyana ba," a cewarsa.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an debe gawarwakin mutanen uku ne cikin dare daga wani gidan kankara a Misrata inda aka ajiye su domin jama'a su rinka kalla.

Wani mai gadi a gidan kankarar ya tabbatar da debe gawarwakin ga gidan talabijin din Larabci na al-Jazeera.

"Ankinmu ya kare," a cewar Salem al Mohandes. "Jami'an sojin Misrata sun dauke Gaddafi zuwa wani wuri da bamu sani ba. Ban sani ba ko sun binne shi ko kuma a'a."

Wakilan sashin talabijin na kamfanin dillancin labarai na AP, sun ce sunga wasu motoci uku suna barin gidan kankarar a ranar Litinin da daddare, kuma da suka shiga gidan daga bisani sai suka taras babu gawarwakin.

Karin bayani