An kai karar gwamnatin tarayyar Najeriya

Image caption Gwamna Sule Lamido na Jigawa

Rahotannin na cewa gwamnonin Najeriya sun shigar da kara a gaban kotun kolin kasar, inda suka bukaci ta hana gwamnatin tarayya cire dala biliyan daya daga cikin asusun rarar man fetur din kasar.

Gwamnatin tarayyar dai ta ce za ta cire kudin ne domin sakawa a wani asusu na musamman da gwamnatin ta amince da kafawa, wanda ake kira Sovereign Wealth Fund a turance.

A makon jiya ne dai Ministar ma'aikatar kudin kasar, Ngozi Okonjo Iweala, ta ce gwamnonin sun amince a rika cire kudi daga asusun rarar man fetur din don sanyawa a asusun Sovereign Wealth Fund.

Ta ce za a cire kudin ne don alkinta su musamman ganin cewa tattalin arzikin kasar na tabarbarewa.