An rufe Gaddafi, dansa na gudun tsira

Wani jami'i a Niger ya ce an ga, dan Kanar Gaddafin da har yanzu ba a san yadda yayi ba, wato Saif al-Islama kusa da kan iyaka da Libya, kuma yan kabilar Azbinawa ne ke taimaka masa.

Kotun manyan laifuka ta duniya dai na neman Saif al-Islam.

An fahimci cewar dan uwansa al-saadi Gaddafi ya nemi mafaka a Nijar cikin watan da ya wuce, a inda gwamnati ta ce, ba za a mayar da wakilan tsohuwar gwamnatin Libyar ba tare da samun tabbacin kariyarsu ba.

Tun farko jami'an sabuwar Gwamnatin Libyar na majalisar wucin gadi sunce, an rufe gawar Kanar Gaddafi da ta dansa, Mutassim a wani wurin sirri cikin hamadar Libya.

An ajiye gawar dai don jama'a su gani a Misrata har ya zuwa ranar litinin.