Ennahda ta soma tattaunawar yin kawance a Tunisia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Ennahda, Rashid Ghannouchi

Jam'iyyar masu ra'ayin Islama a Tunisia, ta Ennahda na tattaunawar yin kawance da jam'iyyu biyu na masu ra'ayin sauyi da ba ruwansu da addinin a harkokinsu domin kafa gwamnatin wucin gadi.

Hakan na zuwa ne yayin da aka bayyana sakamakon zaben farko da aka yi cikin 'yanci a kasar.

Hukumar zaben kasar ta tabbatar da cewa jam'iyyar Ennahda na kan gaba sosai, amma ba a tsammanin za ta samu rinjaye gaba daya.

Jama'ar kasar Tunisia dai sun kada kuri'ar zaben majalisar dokokin kasar da za ta rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar tare da zabar shugaban rikon kwarya da pirayim minista.

An haramta jam'iyyar Ennahda a lokacin mulkin hambararren shugaban kasar, Ben Ali.

Jam'iyyar Ennahda ta sha alwashin goyan bayan demokradiyya mai jam'iyyu barkatai.