Ana jiran sakamakon zaben Tunisia

Hakkin mallakar hoto Reuters

Nan gaba a yau ne za a bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a Tunisia, wanda ke nuna jam'iyyar Ennahda mai kishin Islama ake saran ta samu mafi yawancin kuri'un da aka kada.

Sai dai har jam'iyyar ta yi shelar lashe zaben

Babbar jam'iyyar da ke hamayyar da ita, wato PDP mai son raba addini da mulki, ta amince ta sha kaye.

Sai dai kuma jam'iyyar Ennahda, wadda aka haramta a zamanin mulkin hambararan shugaban kasar, Zine el Abidine Ben Ali, ba za ta samu cikakken rinjaye ba a majalisar.