Ana ci gaba da aikin agaji a Turkiyya

Image caption Ma'aikatan agaji a Turkiyya

Ma'aikatan agajin gaggawa a gabashin Turkiyya sun yi ta aiki a cikin daren jiya Litinin domin lalubo mutanen da suka tsira daga girgizar kasar da aka yi ranar Lahadi.

Dubun dubatar mutane dai sun rasa gidajensu, inda suka shafe dare na biyu a waje.

Akalla mutum dari biyu da saba'in ne suka hallaka sakamakon girgizar kasar, kuma fiye da mutune dubu daya ne suka samu raunuka.

Har yanzu kuma ba a san inda wasu daruruwan mutanen suka shiga ba, a garuruwan Ercis da Van.